Yadda Kotu ta ɗaura aure wata kotu ta raba a Kaduna
Latsa hoton sama domin sauraren rahoton Ibrahim Isa
Wani rikicin aure mai sarƙaƙiya a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ya kai ga tsare uban amarya da wani alƙalin kotun shari'ar Musulunci da ya ɗaura mata aure.
An yi zargin cewa an ɗaura mata aure ne a kan aure, inda aka gwabza shari'a tun daga matakin karamar kotu a Kaduna har ta kai ga babbar kotu har zuwa kotun daukaka ƙara.
Sai dai amaryar da iyayenta sun musanta zargin an ɗaura mata aure kan aure, inda suka ce aurenta na farko ya kai shekara biyu da mutuwa.
Matar mai suna Nasiba 'yar wani shahararren attajiri ne a Kaduna wanda aka fi sani da ASD (Alhaji Sani Dauda), wadda aka ɗaura mata aure da wani mai suna Abubakar Musa Abubakar.
Yarinyar da iyayenta sun nemi a raba auren amma bangaren miji kuma na cewa ba shi da niyyar rabuwa da matarsa.
Amaryar ta shaida wa BBC cewa aurensu ya mutu shekaru biyu da suka gabata inda tuni ta gama idda.
"Aurena da shi babu domin sai da aka sa na rantse da Al-Kur'ani har alƙalin ya zartar da hukunci aka gabatar min da shaidar mutuwar aure."
Da wannan shaidar ne aka dogara wajen ɗaura mata sabon aure da wani mijin. Amma ba a jima ba sai `yan sanda suka kama magabatanta, ciki har da mahaifinta da alƙalin kotun da ya daura mata aure, mai suna Murtala Nasir.
Alƙali Nasir wanda ya tabbatar wa BBC ya ɗaura wa yarinyar sabon aure bayan ganin shaidar mutuwar aurenta na farko, ya ce wannan ne dalilin da ya sa 'yan sanda suka kama su.
Sai dai a cewar mijin yarinyar na farko Abubakar Musa Abubakar, kamar yadda lauyansa, Barista Safyan Saidu Tambai ya bayyana, an ɗaura auren ne a kan aurensa, saboda an soke hukuncin kotun da ta kashe auren, kuma akwai shari'a cikin shari'a da ya dabaibaye auren.
"Kotun sama ta soke hukuncin kotun farko da ta kashe aurenta don haka ta dawo a matsayin matar Abubakar," in ji Barista Tambai.
Babu dai wani martani daga rundunar 'yan sandan jihar Kaduna kan zargin kama iyayen yariyar da kuma alƙalin da ya ɗaura mata sabon aure.