Kalli hotunan baburan da ake fasa kwaurin shinkafa da su

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta kulle kan iyakokinta na tudu, har yanzu ana fasa kaurin kaya daga kasashe makwabta zuwa Najeriyar.

Fasa kwauri
Bayanan hoto, Daya daga cikin matasan garin na Kwangalam na karamar hukumar Mai'aduwa a jihar Katsina yana zaune bisa babur din da yake amfani da shi wajen fasa kwaurin kaya daga Nijar zuwa Najeriya.
Wasu daga cikin baburan da ake amfani da su wajen fasa kwaurin kaya daga Nijar zuwa cikin Najeriya.
Bayanan hoto, Tun bayan da Najeriya ta rufe bakin iyakokinta na tudu watanni biyu da suka gabata a wani yunkuri da ta ce ta yi ne domin magance fasa-kwaurin kayayyaki, musamman shinkafa da kuma dakile satar shigar da makamai, dubban mutane ne 'yan kasar da na makwabtan kasashe da suka dogara ga shige da ficen kayayyaki a iyakokin ke ci gaba da kokawa.
Fasa kwauri
Bayanan hoto, Al'ummomi musamman matasa da ke garuruwan da ke kan iyakokin kasar na daga cikin wadanda ke cin moriyar wannan kusanci, inda wasu ke tafiyar da harkokin safarar kaya ta ka'ida wasu ko, ke fasa-kwauri. Wannan babur din sabo ne, amma tuni an sauya fasalinsa domin ya iya daukar kaya masu nauyi kamar buhunan shinkafa.
Fasa kwauri
Bayanan hoto, Yadda a ke bankara sidin babura domin su iya daukar kaya ba tare da sirdin ya danne tayar baya ba.
Babur
Bayanan hoto, Wani wuri da masu baburan na simoga ke taruwa