Kalli hotunan gobarar kasuwar Balogun a Legas

An tafka babbar asara ta miliyoyin kudi sakamakon gobarar da ta tashi ranar Talata a kasuwar Balogun da ke birnin Legas na Najeriya.

Kasuwar Balogun
Bayanan hoto, Wasu dogayen benaye da wuta ta ci a kasuwar Balogun da ke Legas sakamakon tashin gobara a kasuwar ranar Talata
Bologun
Bayanan hoto, Yadda ma'aikatan hukumar kashe gobara ta jihar ta Legas suka yi kokarin tona kayan da suka kone domin zuba wa wurin ruwa
Bologun
Bayanan hoto, Hayaki ya turnuke a yayin gobarar
Bologun
Bayanan hoto, Wani dogon gini da wutar ta shafa, inda masu kashe wuta ke amfani da motoci masu mika mutum sama
Bologun
Bayanan hoto, Ma'aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Legas suna kokarin kashe gobarar
Bologun
Bayanan hoto, Wani bangare na kasuwa da wutar ta ci
Bologun
Bayanan hoto, Wani jami'in kashe gobara yana gyaran tiyon ruwa
Balogun
Bayanan hoto, Lokacin da jami'an kwana-kwana suka isa kasuwar Balogun domin kashe gobarar a ranar Talata
Balogun
Bayanan hoto, Wasu 'yan kasuwa ke nan da suka yi cirko-cirko lokacin da wutar ke cin shagunansu
Balogun
Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara tare da 'yan kasuwa a kasuwar ta Balogun Market
Balogun
Bayanan hoto, Masu aikin kashe wuta na fesa ruwa da mesa
Balogun
Bayanan hoto, Lokacin da wasu 'yan kasuwa suke fafutukar kwashe kayansu domin gudun ka da wutar ta shafe su
Balogun
Bayanan hoto, Masu aikin kashe wuta na bi sako da loko na kasuwar domin kashe wutar