Hotunan bikin Diwali na Indiya

Diwali biki ne da mabiya addinin Hindu ke yi wanda ke alamta "tasirin haske kan duhu, halin kwarai kan mugunta da ilimi kan jahilci". Ana kwashe kwanaki 5 ana bikin inda mabiya addinin Hindu a Indiya da Nepal ke yi.

Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ran jajiberin bikin Diwali, mutane sun kunna fitilu a Kiritipur don murnar zagayowar ranar bikin.
Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani matashin malamin addinin Hindu dan kasar Nepal ya riko kayan sadakar da zai bai wa Sa lokacin bikin Diwali a Katmandu kasar Nepal ranar Litinin 28, 2019.
Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane suna kona banga lokacin bukukuwan Diwali a Sector 34 ran 27 ga October, 2019 a Noida, Indiya.
Bikin Diwali

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An kunna fitilu a bakin kogin saryu ran jajiberin Diwali a Ayodhya
Bikin Diwali a Indiya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan karon kuwa, mutane sun kunna fitilu miliyan biyar da rabi da fatan shiga littafin Guiness Book of World Records
Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Nepal sun daura wani zare mai 'tsarki' a jikin jelar wani Sa lokacin bikin Diwali a Kathmandu ranar Litinin 28, 2019.
Bikin Diwali a Indiya

Asalin hoton, Hindustan Times

Bayanan hoto, Mutane suna kona banga lokacin bukukuwan Diwali a Sector 34 ran 27 ga October, 2019 a Noida, Indiya.
Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tarkace a titin Kavi Nagar bayan da mazauna garin suka yi shagulgulan bikin Diwali ran 28 ha Oktoba a Ghaziabad da ke Indiya.
Bikin Diwali a Indiya

Asalin hoton, Hindustan Times

Bayanan hoto, Hazo ya lullube birnin New Delhi a Indiya, wayewar gari bayan shagulgulan Diwali ran 28 Oktoba, 2019. Mutane sun yi ta kunna wasu tsinkaye masu tartsatsin wuta a birnin wanda kuma hayakin ya gurbata iska.
Bikin Diwali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bukukuwan Diwali a garin Ayodhya