Kalubalen da na fuskanta a matsayin dan kwallo mata-maza
Ku latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
An haife James Johnson mata-maza, inda ya fara buga wasan kwallon kafa a matsayin mace, a lokacin sunansa Iyabode Abade.
Har ya kai matsayin ya yi wasa a kungiyar kwallon kafa ta kasa, amma aka kore shi bayan sun gane cewa shi mata-maza ne.
Bayan ya ta fuskantar kalubale, da ya kai shekara 19 sai ya yanke hunkucin a yi mishi tiyata wanda zai mayar da shi namiji baki daya.
Hakan ya sa ya sauya sunansa zuwa James Johnson.