Hotunan yadda ake bikin Babbar Sallah a Najeriya

Musulmin Najeriya suna ci gaba da gudanar da bukukuwan Babbar Sallah kamar sauran takwarorinsu da ke sassan duniya daban-daban.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk gabanin sallar idi a Daura ranar Lahadi

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (daga dama) tare da Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk (a tsakiya) gabanin fara sallar idi a Daura ranar Lahadi
Babbar Sallah

Asalin hoton, DG Media KN

Bayanan hoto, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II lokacin da yake jagorantar sallar idi a Kano
Babbar Sallah

Asalin hoton, Kebbi State Government of Nigeria

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu (a tsakiya) lokacin sallar idi a jihar Kebbi ranar Sallah
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal tare da Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III a masallacin idi ranar Lahadi

Asalin hoton, Shamsudeen Umar Maiakwai

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal tare da Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III a masallacin idi ranar Lahadi
Babbar Sallah

Asalin hoton, Lagos State Goverment

Bayanan hoto, Jagoran jam'iyyar APC Bola Tinubu (na biyu daga hagu) a masallacin idi na Dodan Barracks a jihar Legas ranar Sallah
Babbar Sallah

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Mata ma suna cikin wadanda suka halarci sallar idin a Daura
Shugaba Buhari yayin da yake yanka ragonsa a Daura jim kadan bayan sallar idi

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yayin da yake yanka ragonsa a Daura jim kadan bayan sallar idi
Babbar Sallah

Asalin hoton, The Governor of Kaduna State

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai lokacin da yake yanka ragonsa a karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna ranar sallar
Shugaban kasar Guinea Alpha Condé

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Shugaban kasar Guinea Alpha Condé (wanda yake ziyara a Najeriya) lokacin da aka nada shi Talban Daura wanda Sarkin Daura ya yi masa bayan sallar idi a Daura
Babbar Sallah

Asalin hoton, Shamsudeen Umar Maiakwai

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal lokacin da ya kai gaisuwar Sallah a fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III jim kadan bayan kammala Sallar Idi a Sokoto
An yi kwarya-kwaryar hawan sallah a Daura bayan sallar idi a ranar Lahadi

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Hakazalika an yi kwarya-kwaryar hawan sallah a Daura bayan sallar idi a ranar Lahadi
Babbar Sallah

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Bayanan hoto, Sai dai wasu 'yan kasar sun koka da yadda farashin raguna ya yi sama a bana