Sulhu tsakanin 'yan banga da Fulani ya yi nasara a Zamfara – Matawalle

Bayanan bidiyo, Sulhu tsakanin 'yan banga da Fulani ya yi nasara a Zamfara - Bello Matawalle

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi karin haske kan sulhun da ya ce an fara yi tsakanin 'yan bindiga da Fulani domin kawo karshen rikicin da ya addabi jihar.

Rikicin, wanda aka dade ana yi, ya yi sanadiyyar mutuwa tare da sace mutane da dabbobi da dama.

Amma Gwamna Matawalle ya ce a yanzu an yi musayar sama da mutum 150 tsakanin Fulani da 'yan banga, kuma tuni aka fara bude wasu kasuwanni da suka shafe shekara uku ba a rufe.