Jummai Ibrahim: Matar da ta haifi 'ya'ya 17

Bayanan bidiyo, 'Yadda na haifi 'ya'ya 17'

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Ranar Alhamis 11 ga watan Yuli aka yi bikin Ranar Yawan Al'ummar Duniya, inda a bana adadin al'ummar duniya ya kai 7.7 biliyan.

Mun zanta da wata mata mai suna Jummai Ibrahim wadda ta haifi 'ya'ya 17.

Jummai wadda take zaune a Kano, ta ce yanzu 'ya'ya 10 ne kawai cikin 17 suke raye.