Buba Galadima: APC ba ta isa ta kore ni ba

Bayanan bidiyo, Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu fa shi dan jam'iyya mai mulki ne ta APC

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu shi dan jam'iyya mai mulki ne ta APC domin kuwa yana daya daga cikin mutum tara da suka kafa ta.

Sannan kuma ya ce ya goyi bayan jam'iyyar adawa ta PDP ne saboda sun yi hadaka da ita.