Yadda dinkin sallar bana ya kasance a Kano
A yayin da ya rage 'yan kwanaki a fara gudanar da bukukuwan karamar sallah a fadin duniya, jama'a da dama a Najeriya na ta haramar tanadin shagulgulan sallar ta hayar dinka sababbin kaya ga wanda ya sami wadata.
A wasu lokuta teloli kan bar wasu mutanen da saka tsohon kaya saboda rashin kammala dinkin.
Abokin aikin mu da ke Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci wasu shagunan teloli don ganin yadda suke ciki da dinkunansu da kuma yadda ciniki ya kaya a wannan shekarar, ga kuma tattaunawarsu da wasu teloli har ma da masu kaya.