Za a yi karancin abinci a jihohin da ake satar mutane — Masari
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar da BBC ta yi da Gwamna Masari:
A yayin da ake ci gaba da fargabar yadda rashin tsaro ke barazana ga noman bana a yankunan da ke fama da garkuwa da mutane a Najeriya, gwamman jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce babu makawa za a sami karancin abinci a yankunan.
Gwamna Masari ya bayyan haka ne a yayin wata hira da BBC ta yi da shi.
A cikin hirar, gwamnan ya tabo batuwa da dama da suka shafi tsaro a yankunan jiharsa da ma na makwabta, ciki har da batun irin kokarin da gwamnatocin yankunan ke yi wajen kawo karshen hare-hare da ma satar mutane da ake yi.