Mike Zhang: Hotunan nadin sarautar Wakilin 'Yan China a Kano

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya nada wani dan China, Mista Mike Zhang, a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano ranar Alhamis.

Mike Zhang bayan an nada shi a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano
Bayanan hoto, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ne ya nada Mista Mike sarautar a fadarsa ranar Alhamis
Hotunan nadin Mike Zhang
Bayanan hoto, Dimbin jama'a ne suka halarci taron nakin sarautar
Mike Zhang
Bayanan hoto, Mike Zhang ya shafe shekara 17 yana harkokin kasuwanci a Kano, kuma shi ne wanda ya mallaki kamfanin ruwan roba na Maya a Kano
Hotunan nadin Mike Zhang a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano
Bayanan hoto, Sarkin ya ce ya nada shi sarautar ne saboda "kokarinsa wajen habbaka" kasuwanci a Kano
Hotunan nadin Mike Zhang a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano.
Bayanan hoto, Sarkin ya ce yana fatan nadin zai kara karfafa masa gwiwa
Wakilin 'yan China
Bayanan hoto, Ana saran Mista Zhang zai rika halartar zaman fada da kuma sukuwa lokacin hawan sallah
'Yan China
Bayanan hoto, Cikin mutanen da suka samu damar halartar taron nadin sarautar har da 'yan uwansa 'yan China
Hotunan nadin Mike Zhang a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano.
Bayanan hoto, Har ila yau Sarkin ya ce yana fatan Mista Zhang zai zama" idonsu" tsakanin 'yan kasuwan Kano da 'yan China
Hotunan nadin Mike Zhang a matsayin Wakilin 'Yan Chinan Kano.
Bayanan hoto, Akwai dimbin 'yan China da suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar