Hotunan halin da ake ciki a Sudan

Jama'a sun ci gaba da nuna turjiya a sassan kasar Sudan bayan da sojoji suka hambare gwamnatin Omar al-Bashir, kuma sun ce za su mulki kasar na shekara biyu.

The day before, an icon of the protests, Alaa Salah, who has been nicknamed the "Nubian queen", speaks to crowds in Khartoum.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ita ce Alaa Salah, wadda ake kira da sunan "Sarauniyar Nuba", wadda ta kasance wata muhimmiyar alamar turjiya ga masu zanga-zanga a Sudan.
Members of the Sudanese military gather in a street in central Khartoum on April 11, 2019, after one of Africa's longest-serving presidents was toppled by the army.

Asalin hoton, AHMED MUSTAFA

Bayanan hoto, Wani sojan Sudan a tsakiyar birnin Khartoum tare da wasu fafaren hula na nuna farin cikinsa kan hambare Shugaba Omar Hassan al-Bashir daga mulki.
A wannan hoton ana iya ganin wani dan Sudan na nuna murnarsa a gaban shalkwatar sojojin Sudan da ke Khartoum.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan hoton ana iya ganin wani dan Sudan na nuna murnarsa a gaban shalkwatar sojojin Sudan da ke Khartoum.
Sudanese demonstrators gather in a street in central Khartoum on April 11, 2019, after one of Africa's longest-serving presidents was toppled by the army

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba a bar mata a baya ba. Nan hoton wasu 'yan mata ne a birnin Khartoum suna nuna alamar nasara bayan da labari ya zo masu cewa an hambare Omar al-Bashir daga mulki.
Wannan hoton wani dan Sudan ne a Khartoum yana sumbatar wani sojan kasar bayan da sojoji suka hambare Omar al-Bashir daga mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hoton wani dan Sudan ne a Khartoum yana sumbatar wani sojan kasar bayan da sojoji suka hambare Omar al-Bashir daga mulki.
A nan kuma wani soja ne tare da wani farar hula suna nuna murnarsu da labarin hambare Shugaba al-Bashir daga mulki a Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuma wani soja ne tare da wani farar hula suna nuna murnarsu da labarin hambare Shugaba al-Bashir daga mulki a Sudan.
Yadda 'yan Sudan suka fita bisa titunan birnin Omdurman na kasar Sudan kenan suna murnar hambareal-Bashir daga mukaminsa na shugaban kasa bayan ya shafe shekara 30 yana mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda 'yan Sudan suka fita bisa titunan birnin Omdurman na kasar Sudan kenan suna murnar hambare al-Bashir daga mukaminsa na shugaban kasa bayan ya shafe shekara 30 yana mulki.
Matasa da sauran jama'a na ci gaba da nuna farin ciki da samun biyan bukata bayan hambare al-Bashir daga mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasa da sauran jama'a na ci gaba da nuna farin ciki da samun biyan bukata bayan hambare al-Bashir daga mulki.
Yadda 'yan Sudan suka fita kwansu da kwarkwatarsu domin nuna adawa da mulkin Omar al-Bashir a Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda 'yan Sudan suka fita kwansu da kwarkwatarsu domin nuna adawa da mulkin Omar al-Bashir a Sudan.
Nan ma yadda 'yan Sudan suka dare bisa tankunan yaki a shalkwatar sojojin Sudan a birnin Khartoum inda suke murnar hambare al-Bashir daga mukaminsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma yadda 'yan Sudan suka dare bisa tankunan yaki a shalkwatar sojojin Sudan a birnin Khartoum inda suke murnar hambare al-Bashir daga mukaminsa.
Nan ma sojojin Sudan ne a birnin Khartoum inda suke murnar hambare al-Bashir daga mukaminsa tare da daruruwan dubban mutane.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma sojojin Sudan ne a birnin Khartoum inda suke murnar hambare al-Bashir daga mukaminsa tare da daruruwan dubban mutane.