'Rana mafi muni' a New Zealand
A kalla mutum 49 ne aka kashe kuma sama da 20 suka samu raunuka masu muni bayan da aka kai hari a masallatai biyu a Christchurch da ke New Zealand.
An kama mutum hudu da ake zargi suna da hannu a harin- an bayyana daya daga cikinsu dan kasar Ostireliya a matsayin mai tsattsauran ra'ayin ta'addanci.
Shugabanni da mutanen duniya sun yi Allah-wadai da harin inda gwamnatin kasar ta sha alwashin hukunta maharan.
Gwamnatin New Zealand ta shawarci musulmai da su kulle masallatansu har sai baba ta gani.