Iyaye sun yi zanga-zangar bacewar 'ya'yansu a Borno

Bayanan bidiyo, Sun ce sojoji ne suka dauke musu yara fiye da shekaru 5 da suka wuce

Mata sun yi zanga-zanga don neman sanin inda 'ya'yansu suke tun bayan da sojoji suka kama su shekara shida da suka wuce, a cewarsu.

Sun yi zanga-zangar ne a karamar hukumar Jere ta jihar Borno a ranar Alhamis.