Muhawarar jihar Kano: Kalli hotunan birnin Kano

Kano ne gari na biyu mafi girma a Najeriya, kuma cibiyar kasuwanci a arewacin kasar.

Matsugunin Jami'ar Yusuf Maitama Sule (Gidan Ado Bayero) a Kofar Nasarawa
Bayanan hoto, Matsugunin Jami'ar Yusuf Maitama Sule (Gidan Ado Bayero) a Kofar Nasarawa
Tun dawo wa mulkin siyasa a 1999 daga mulkin soja, garin Kano ya samu bunkasa da ci gaba ta hanyar raya garin da tituna da gadoji
Bayanan hoto, Tun dawo wa mulkin siyasa a 1999 daga mulkin soja, garin Kano ya samu bunkasa da ci gaba ta hanyar raya garin da tituna da gadoji
Gadojin sun taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a garin Kano
Bayanan hoto, Gadojin sun taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a garin Kano
Wata sabuwar doguwar gada da ake dab da budewa a birnin Kano
Bayanan hoto, Wata sabuwar doguwar gada da ake dab da budewa a birnin Kano
Tun dawo wa mulkin siyasa a 1999 daga mulkin soja, garin Kano ya samu bunkasa da ci gaba ta hanyar raya garin da tituna da gadoji
Bayanan hoto, Tsohuwar gwamnatin Kano ce ta fara aikin gina gadar, gwamnati mai ci kuma ta karasa aikin
Kasuwar waya a Kano
Bayanan hoto, Kasuwar sayar da wayoyi ta Farm Centre
Sayar da waya da gyaranta sun zama babbar sana'a ga dubban mutane musamman matasa
Bayanan hoto, Sayar da waya da gyaranta sun zama babbar sana'a ga dubban mutane musamman matasa a jihar
Hada-hadar sayar wayar salula da kayanta da kuma gyara sun taimaka wajen rage zaman kashe wando ga matasa
Bayanan hoto, Hada-hadar sayar da wayar salula da kayanta da kuma gyara sun taimaka wajen rage zaman kashe wando ga matasa