Adikon Zamani: Yadda 'yan Arewa ke bara a Lagos

Bayanan sautiAdikon Zamani

A gabaki dayan Lagos, a wuraren ba da hannu da tituna da kasuwanni, duk masu bara ne suka mamaye ko ina.

Hakan dai ba bakon abu ba ne a manyan birane kamar Lagos.

Sai dai abin mamaki shi ne yawancin masu barar hausawa ne daga arewancin Najeriya. Za ku ga 'yan mata rike da yara masu jin yunwa, suna bara.

Wani lokaci kuma sai ku ga mata tsofaffi masu nakasa da wadanda ba su da nakasa suna kwankwasa tagar motocin mutane suna bara.

Me ya sa mutanenmu sun fi kowa bara?

Bincikenmu ya nuna cewa bara kasuwanci ne mai kyau ga wadansu mutane.

Yana kawo wa masu yi kudi sosai da har mutane na bada hayar 'ya'yansu don a je bara da su.

Yankin Agege, gefen layin jirgin kasa wuri ne na talakawa. Nan ne matattrar makafi da kurame da guragu da kutare da ma sauran masu nakasa.

Babu wani abin a zo a gani a rayuwar da suke, amma tamkar suna farin ciki da ita.