Hotunan yadda zaman majalisar Kano da wakilin Ganduje ya kasance

Ga wasu daga cikin hotunan yadda zaman majalisar Kano da wakilin Ganduje ya kasance da aka yi a ranar Juma'a. Abokin aikinmu Ibrahim Isa ne ya dauko mana su.

Wannan ita ce kujerar da a ka shirya don gwamna Abdullahi Ganduje ya zauna a kanta
Bayanan hoto, Da dama al'ummar da ta taru a zauren majalisar dokokin jihar Kano ta yi tsammanin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje zai je da kansa ba sako ba. Wannan ita ce kujerar da a ka shirya don gwamna Abdullahi Ganduje ya zauna a kanta
Majalisar ta gayyaci gwamna ganduje domin ji daga bakinsa kan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa
Bayanan hoto, An dakanci isar gwaman har zuwa bayan karfe goma na safe da wasu 'yan mintoci, wato lokacin da kwamitin ya tsara don fara zaman.
Wannan shi ne hoton daya daga cikin mambobin kwamitin a yayin da ya ke magana
Bayanan hoto, Wannan shi ne hoton daya daga cikin mambobin kwamitin a yayin da ya ke magana
Wannan shi ne wanda ya wakilci Ganduje, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Malam Muhammadu Garba
Bayanan hoto, Amma kwatsam sai ala ga kwamishin watsa labarai, Mallam Muhammad Garba ya shiga zauren tare da lauyan Gwamna, Barrister Ma'aruf Yakasai, inda ya sanar da kwamitin cewa ya je ne ya wakilci gwamna, kasancewar gwmnan yana da zabin zuwa da kansa ko kuma a wakilce shi, inda bai tsaya wata-wata ba ya gabatar da bahasin gwamna a rubuce, wadda ya danka wa kwamitin bayan ya karanta, yana musanta zargin da ake yi wa gwamnan na karbar rashawa.
Wadannan sune 'yan kwamitin majalisar
Bayanan hoto, An tsaurara tsaro sosai a majalisar saboda sa ran zuwan gwamnan, ciki har da jami'an da ke dauke da na'urorin da ke sansanar boma-bomai.
Kwamitin wanda ke karkashin Baffa Babba Danagudi ya ce zai je ya yi nazarin bidiyon
Bayanan hoto, Kwamitin ya bayyana kasancewar ya saurari bangarori biyun, wato da dan jaridar da ya wallafa hotunan bidiyon da kuma wanda ake zargi, yanzu kuma zai mayar da hankali ne wajen nazarin hotunan kafin ya dauki mataki na gaba.
Tun da safiyar juma'ar yau ne 'yan jarida da kungiyoyin al'umma da kuma 'yan kallo suka hallara a harabar majalisar, ana dakon zuwan gwamnan
Bayanan hoto, Kwamitin majalisar dokokin dai na da babban kalubale a gabansa, kasancewar kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da al`umomin jihar Kano da wajen jihar da dama sun zuba masa ido wajen ganin ya kamanta adalci, kamar yadda ya yi alkawari.
'Yan jarida na daukan bidiyo ta hotunan taron
Bayanan hoto, 'Yan jarida da kungiyo daban-daban sun halarci zaman.
Wakilin gwamnan ya ce gwamna yana da zabi ya je da kansa ko kuma ya tura wakili
Bayanan hoto, Yayin da kwamitin ke fuskantar matsalin-lamba daga wasu da ke zargin cewa 'yan kwamitin 'yan-koren gwamnati ne don haka da wuya su dauki matakin da zai bakanta ran gwamna!