Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Kaduna ya shafa

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a cikin garin Kaduna da kewaye sakamakon rikicin addini da kabilanci da ya barke a jihar a ranar Lahadi.

Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i lokacin da ya je duba wadanda suka jikkata a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna ranar Litinin
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka jikkata bayan barkewar sabon rikicin a ranar Lahadi
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da sabon rikicin
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, An samu tashin hankali a wasu yankuna na garin Kaduna da Marabar Rido da kuma wasu unguwanni a tsakiyar birnin
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Gwamna el-Rufai lokacin da ya je duba wandansu wuraren da abin ya shafa a garin Kaduna
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Wani wuri da sabon rikicin ya shafa a garin Kaduna
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, Gwamna el-Rufa'i tare da wadansu jami'an tsaro lokacin da suka je garin Kasuwar Magani, wurin da aka fara rikicin a ranar Alhamis
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/Samuel Aruwan

Bayanan hoto, A makon jiya ne aka samu tashin hankali a garin Kasuwar Magani da ke yankin karamar hukumar Kajuru, abin da ya haifar da asarar rayuka fiye da 50
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Twitter/The Governor of Kaduna State

Bayanan hoto, Gwamna el-Rufa'i lokacin da yake taron da samu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a jihar ranar Litinin
Rikicin jihar Kaduna

Asalin hoton, Twitter/The Governor of Kaduna State

Bayanan hoto, Gwamna el-Rufa'i lokacin da ya kai ziyara unguwar Rigasa don kwantar da hankulan al'ummar unguwar a ranar Litinin