Hotunan barnar da guguwar Michael ta yi a Amurka

Guguwar da aka yi wa lakabi da guguwar Michael ita ce ta uku mafi girma a tarihin Amurka.

Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fiye da mutane 370,000 a jihar Florida aka yi wa gargadi da su bar gidajensu amma su ka yi burus da gargadin.
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Guguwar ta lalata gidaje da masana'antu saboda karfinta
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Lardin Seminole da ke Georgia, iskar ta rusa wani gida da yarinya 'yar shekara 11 a ciki kuma ta mutu.
Guguwar Michael

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane biyu, har da karamin yaro sun mutu bayan da baraguzai suka fado musu.
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu gine-gine a jihar Florida ba su da karfin daukar guguwar
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shaguna da dama sun lalace, rufinsu da taguna sun farfashe
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wasu sassan garin, mutane suna fi ta cikin ruwan da ya yi ambaliya bayan da guguwar ta rasa yankunan da suke.
Guguwar Michael

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Guguwar ta tunbuke bishiyoyi da dama daga jijiyoyinsu