Fasto ya nemi afuwa bisa taba maman mawakiya Ariana Grande

Asalin hoton, Getty Images
Limanin cocin da ya jagoranci jana'izar mawakiya Aretha Franklin ya nemi afuwar shahararriyar mawakiyar nan Ariana Grande bayan da aka zarge shi da latsa mamanta a kan dandamali.
Hotuna sun nuna Bishop Charles H Ellis III ya rike kugun Ariana inda dan yatsansa ya rika latsa mamanta.
Sai dai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na the Associated Press cewa "ba ni da niyyar taba maman ko wacce mace."
"Watakila na wuce gona da iri, watakila kuma na nuna matukar abota da shakuwa, amma ina neman afuwa," in ji shi.
Malamin cocin ya ce yana rungumar dukkan mawaka, maza da mata, a lokutan bukukuwa.
Sai dai mutanen da suka kalli jana'izar a talbijin sun rika wallafa hotuna lokacin da Ariana ta mike tsaye domin rera wakar Aretha msai suna (You Make Me Feel Like) A Natural Woman.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Mutane da dama na ganin Bishop Ellis ya yi azarbabin sanya hannunsa inda bai dace ba lokacin da yake magana da mawakiyar mai shekara 25 - suna masu cewa da alama ba ta ji dadin yadda ya rike jikinta ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kazalika wasu sun soki Ariana saboda sanya tufafin da ba su dace ba zuwa coci, suna masu cewa tufafin dangalallu ne.