Ina nan a jam'iyyar APC daram-dam – Wamakko
A yanzu ta bayyana a fili cewa akwai sabani tsakanin gwamnan jihar Sakkwato aminu Tambuwal da wanda ya gada Sanata Aliyu Wamakko, har ma sun raba jam'iyya.
Gwamna Tambuwal ya fita daga APC zuwa PDP, yayin da shi kuma Sanata Wamakko ya ce yana nan daram a jam'iyyar APC.