Rayuwar Fulanin da suka mayar da kudancin Najeriya gida

BBC ta kai ziyara rugar Fulani ta Nyama a kudu maso gabashin Najeriya, inda ta gana da wasu Fulani da ba su taba zuwa arewacin kasar ba.

Fulani
Bayanan hoto, Daya daga cikin 'ya'yan Fulani da ke makaranatar sakandare, ke koyawa kannenta 'yan firamare karatu, saboda rashin isassun malamai a makarantar
Fulani
Bayanan hoto, 'Ya'yan Fulanin na rayuwarsu cikin nisahdi a wannan Ruga ta Nyama da ke kauyan Akwuke a jihar Enugu. A nan suna wasa ne bayan tashi daga makaranta
Fulani
Bayanan hoto, Nan shi ne ajin da 'ya'yan Fulanin da ke rugar Nyama ke karatu. Ana koyar da 'yan aji daya har zuwa aji biyar na firamare a karkashin bishiya daya saboda rashin ajujuwa da kuma rashin malamai
Fulani
Bayanan hoto, Wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ke nan ya ke tambayar yaran abin da ake koya musu
Fulani
Bayanan hoto, Duk da wannan yanayi da suke ciki na rashin dakunan karatu da kayan aiki, yaran suna iya kokarinsu wurin koyon karatu da rubutu
Fulani
Bayanan hoto, Sarkin Fulanin na kudu maso gabas da kudu masu kudancin Najeriya Ardo Sa'idu Baso tare da 'ya'yansa da jikokinsa. Ya ce babu abin da ya ke so zuri'arsa su yi kamar karatu
Fulani
Bayanan hoto, Baya ga karatu, yaran na samun damar yin sana'ar da suka gada daga iyaye da kakanni ta kiwo
Wakilan BBC tare da wani Basarake a Enugu
Bayanan hoto, Wakilin BBC AbdusSalam Ibrahim Ahmed daga (hagu), Basarake Igwe Bernard na Nwoye (tsakiya) na Masarautar Akwuki da kuma wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai lokacin da suka kai masa ziyara
Fulani
Bayanan hoto, Masu magana na cewa ba a rasa nono a ruga, haka kuma batun ya ke a wannan rugar Fulanin ta Nyama a jihar Enugu
Yusuf Yakasai
Bayanan hoto, Kuma da alama Yusuf Ibrahim Yakasai ba ya barin tayi, domin kuwa sai da ya sha furar duk da cewa ko "zo" bai iya fada ba da Fullanci.