Abin da ya sa ba na bara – Makaho
Ibrahim Ahmad wani makaho ne da ya ce ya rungumi sana'ar saka duk da larurar rashin gani da ya ke fama da ita.
Ya koyi sana'ar ne domin daukar nauyin bukatunsa da na iyalinsa, saboda yadda yake kyamar bara da ya ce wulkanci ce.
Ibrahim wanda dan asalin jihar Kano ne amma yake zaune a Abuja, ya ce yana iya tantance na'uin abubuwan da ya ke yin sakar da su, duk kuwa da cewa ko kadan ba ya gani.
Yana saka abin sa furanni, da shimfidar da ake sawa a kan teburin cin abinci da wasu kayan sakar.
Sai dai matashin ya ce yana fama da kalubale da suka hadar da rashin jari, da rashin wajen da zai zauna yana sayar da kayan.
A yanzu dai yana rike abin da ya saka ne a hannunsa yana yawon talla a titunan Abuja.