Hotunan yadda kayan marmari ke yin kwantai a Kano

Wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa ya ziyarci kasuwar kayan marmari inda mutane da dama ke kaurace wa sayen kayan saboda tsadar da suka yi a farkon azumi, lamarin da ya sa kayan ke yin kwantai a kasuwa.

Kayan Marmari
Bayanan hoto, Kamar yadda aka sani ne a Najeriya kasuwar kayan marmari irin su lemo da ayaba da dangoginsu kan bude lokacin azumin watan Ramadan. Sai dai a jihar Kano mutane da dama sun kaurace musu sakamakon tsadar da suka yi a farkon shiga azumin.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, Wannan lamari ya sa kayan marmarin yin kwantai a kasuwa, duk kuwa da cewa farashinsa na kara sauka, sakamakon yawaitar da yake yi a kasuwa.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, A Kano, kayan marmarin ya yi wani irin tashin gwauron zabo a makon farko na azumin wannan wata na Ramadan, inda dozin din lemo saffa ya kai naira 250 zuwa 300, sabanin yadda aka saba saye a baya, wato naira 150 zuwa 200.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, Wannan juya-baya da masaya ke yi wa kayan marmari, a bangare guda, ya yi mummunan tasiri a kan kasuwarsa, musamman ma Lemo, kasancewar ya yawaita a kasuwa yayin da masaya ke karanci.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, Duk da cewa farashin kayan ya dan sauka, hankalin mutane da dama bai koma kan kayan marmarin ba.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, Yayin da wasu ke danganta nauyin kasuwar Lemo da sauran kayan marmari da matsin tattalin arziki, wasu 'yan kasuwar kuma na cewa kayan ne ya yi yawa a kasuwa, musamman ma Lemo sakamakon shigowar kakarsa, mako biyu da fara azumi, har ta kai ga yana yin kwantai.
Kayan Marmari
Bayanan hoto, Ko da yake wadannan bayanan ba za su kankare zargin da ake yi ga wasu 'yan kasuwar ba, cewa su kan tsawwala farashi a duk lokacin da watan azumi ya kama, duk kuwa da kiraye-kirayen da malaman addini kan yi musu, kuma irin wannan dogon-burin ne ya kore musu kasuwa.