Hotunan yadda Aisha Buhari ta yi buda baki da shugabannin Mata

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa.

Aisha Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Aisha Buhari ta yi buda baki tare da shugabannin mata a fadar shugaban kasa a ranar Asabar
Aisha Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Buda bakin ya samu halartar mata daga kungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida da kungiyoyin addinai da sauransu.
Buda Baki tare da Aisha Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Daga cikin wadanda aka gayyata buda bakin har da BBC, kuma Raliya Zubairu da Fatima Othman ne suka wakilci BBC
Aisha Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A wajen buda bakin, Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari da uwar gidan mataimakin shugaban kasa sun gabatar da jawabi
Aisha Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A jawabinta, Uwar gidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta yi kira ga mata su tabbatar da zaman lafiya a tsakanin matasa, musamman hadin kan kasa da kuma kwanciyar hankali
b

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto, A nata jawabin, uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo ta ce Azumi na daga cikin hanyoyin yabon Ubangiji ga dukkanin ni’imominsa ga bil’adama. Ta fadi wasu dalilai da dama da ya kamata mutane su godewa ni’imar Mahaliccinsu.
Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto, Baya ga Aisha Buhari da kuma Dolapo Osinbajo, an ba wasu mata damar gabatar da jawabi a wajen buda bakin.
Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto, Wakiliyar BBC Raliya Zubairu na cikin 'yan jaridar da aka ba dama suka gabatar da jawabi.