Hotuna: Buhari ya yi bankwana da Super Eagles

Shugaban Najeriya ya gana da tawagar Super Eagles a fadarsa a Abuja inda ya ma su bankwana a yayin da suke shirin barin kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.

Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da tawagar Super Eagles a fadarsa a Abuja a ranar Laraba.
Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Tawagar Super Eagles ta gana da shugaban ne a yayin da 'yan wasan ke shirin barin kasar zuwa London domin wasan sada zumunci da Ingila a ranar Asabar.
Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Buhari ya yi wa tawagar ta Super Eagles bankwana a yayin da suke shirin barin kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.
Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Tawagar ta kunshi 'yan wasan Super Eagles da kocinsu da kuma shugaban hukumar NFF da Ministan wasanni.
Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Najeriya da ke rukunin D za ta fara wasa ne Croatia a ranar 16 ga Yuni kafin ta fafata da Iceland da kuma Argentina.
Buhari da 'yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Buhari ya bukaci 'yan wasan su taka rawar gani a gasar cin kofin duniya domin alfaharin Najeriya