Yadda mata ke fuskantar matsin lamba su gaggauta yin aure
Mata da dama ne ke bayyana damuwa game da yadda suke fuskantar matsin lamba daga iyayensu kan batun gaggauta yin aure ta ko wane hali tun kafin su kai shekara 30.
Tsananin matsin lambar har ya kai wani lokaci iyaye na cin zarafin 'ya'yansu mata da nufin su ji takaici har su gaji su yi aure.
Yadda wasu iyayen ke nuna kamar ana sayar da mazan aure ne a kasuwa, 'ya'yansu kuma sun ki mallakar nasu.
Shirin na wannan makon ya tattauna ne kan wannan batu musamman halayyar da wasu iyayenmu da ke tilasta wa 'ya'yansu yin aure a lokacin da ba su tashi ba.
Shin ko wannan tabi'a ce mai kyau? Ko kwalliya na biyan kudin sabulu?