Kun san yadda ake haifar mata-maza?

Bayanan sautiKun san yadda ake haifar mata-maza?

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar da Halima Umar Saleh ta yi da Dr Anas Yahaya.

Mata-maza mutane ne da ake haifarsu da al'aurar maza da kuma ta mata.

A wasu kasashen gabashin Afirka, iyayen da suka haifi mata-maza kan dauka cewa an yi musu baki ne, don haka su kan kalli lamarin a matsayin abin kunya ko ma abin neman tsari.

Sai dai a cewar masana akwai bayani a kimiyyance game da yadda halittar mata-maza ke kasancewa.

Dokta Anas Yahaya, kwararren likita ne kuma malami a Sashen Nazarin Halittar Dan-Adam da ke Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce mata-maza halitta ce da ke samuwa sakamakon matsalolin sinadaran da ke taimakawa wajen halitta.

"Alal misali", inji shi, "lokacin da kwan namiji da na mace suka hadu suke ba da halitta ta namiji ko mace, to a lokacin ake samun matsala ta yadda kwan mace kafin ya hadu da na namiji... kan rabe gida biyu; idan aka yi [rashin] sa'a maniyyin namiji guda biyu suka hadu da rababben kwan na mace, shi ke nan sai a samu mata-maza."

Masanin ya kuma ce ba gadon halittar ake yi ba, ko da yake akwai wadansu dalilan da kan haddasa hakan, baya ga rabewar kwan mace kafin haduwarsa da na namiji.

Sannan kuma, a cewar Dokta Yahaya, zai yi wuya a iya gane cewa jaririn da ke ciki mata-maza ne ta hanayr amfani da gwaje-gwajen da aka saba yi wa masu ciki—sai dai ta hanyar wani gwaji na musamman, inda za a debi ruwan cikin mai juna-biyu a auna.