Ko tarukan APC za su raba kan 'ya'yanta?
A wannan makon ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fara gudanar da zabukan sabbin shugabanninta a matakai daban-daban.
Wasu na ganin za a iya samun rikice-rikice a cikin jam'iyyar musamman daga wadanda ba su samu biyan bukata ba, to amma jam'iyyar na cewa kan 'ya'yanta a hade ya ke.