Yadda ake amfani da jakuna a matsayin dakin karatu

Bayanan bidiyo, Yadda ake amfani da jakuna a matsayin dakin karatu

Luis Soriano ya shafe sama da shekara 20 yana amfani da jakunansa Alfa da Beto, wajen safarar littattafai zuwa yara a yankunan karkara a Colombia.

Luis ya dauki wannan matakin ne kasancewar yara 'yan makaranta da dama a yankunan karkara ba su da litattafan da za su yi karatu a gida, musamman idan an ba su aikin gida.