2019: Buhari yana da matsala a Arewa - Buba Galadima
Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki na ganin ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin takara saboda cimma nasarori a wa'adinsa na farko.
To amma wasu 'yan APC da kuma jam'iyyar PDP mai adawa suna ganin babu wani abun a zo a gani da shugaban ya yi a wa'adinsa na farko.
Injiniya Buba Galadima, wanda tsohon na hannun damar shugaban ne, ya ce Buhari na da matsala a arewacin kasar saboda yadda ra'ayoyi suka rabu kan takarar tasa.
Ga wani bangare na tattaunawar bidiyo da aka nada daga shirin Ra'ayi Riga da ake yi duk mako.