Hotunan yadda Buhari ya gana da 'yan Matan Dapchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daliban garin Dapchi da Boko Haram ta sako bayan sace su a ranar 19 ga watan Fabrairu.

'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daliban makarantar garin Dapchi su 107 a fadarsa da ke Abuja.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai da 'yan Matan 105 suka tsabtace hannayensu kafin su shiga fadar shugaban kasa domin gana wa da Buhari.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin 'yan matan da Boko Haram ta sace 'yan aji daya ne na Sakadanre a makarantar Mata a garin Dapchi da ke jihar Yobe yankin arewa maso gabashin Najeriya.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cikin jawabinsa lokacin ganawar, Shugaba Buhari ya shaida daliban cewa za su yi rayuwa cikin 'yanci da cimma burinsu na rayuwa a Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tsoron wani tashin hankali ko cin zarafi ba.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban ya ce sakin matan, bayan da ya umarci jami'an tsaron kasar su tabbatar babu abin da ya same su, "abin farin ciki ne."
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buhari ya shaida wa daliban cewa ya umarci dukkan jami'an tsaro da su yi aiki domin tabbatar da cewa ba a sake ganin irin wannan lamarin ba.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gabatar wa shugaban na Najeriya da 'yan matan ne bayan da aka bincike lafiyarsu tare da kwantar musu da hankali.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari
Bayanan hoto, Dalibai 107 ne dai aka sako kuma 105 daga cikinsu 'yan matan makarantar Dapchi ne da kuma mutum biyu da Boko Haram ta sace.
'Yan Matan Dapchi tare da Buhari
Bayanan hoto, Shugaba Buhari kuma ya sha alwashin ganin an sako daliba daya da ta rage a hannun mayakan Boko Haram da kuma 'yan matan Chibok da aka sace tun 2014