Bidiyon zanga-zangar nakasassu a Abuja
Nakasassu sun gudanar da wata zanga-zanga a majalisar dokokin Najeriya a Abuja, bisa rashin basu kulawa ta musamman wajen daukar aiki. Sun ce suna da masu ilimi da dama a cikinsu da za su iya yin duk wani aikin gwamnati.
Sun ce babu wata kulawa da masu karatu daga cikin su suke samu daga gwamnati.
Bidiyo: Habiba Adamu