Hotunan rayuwa a Dapchi bayan sace 'yan mata

Wasu daga cikin 'yan matan Dapchi da suka tsallake rijiya da baya sun shaida wa BBC cewa ba za su sake zuwa makaranta ba, yayin da wasunsu suka ce ba za su fasa karatu ba komai runtsi.

Dapchi
Bayanan hoto, A ranar 20 ga watan Fabrairu aka fara samun labarin wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun sace dalibai sama da 100 a makarantar mata ta kwana a garin Dapchi da ke cikin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
Dapchi
Bayanan hoto, Fatima Awwal daya daga cikin daliban da suka tsira ta shaida wa BBC cewa a lokacin da aka kai harin duk makarantar ta rikice ana ta guje-guje saboda karar harbe-harben bindigogi da ganin harsasai a sama kamar wuta na yawo.
Dapchi
Bayanan hoto, Matsalar sace 'yan makarantar dai ta kasance matsala da ta shafi kusan kowane gida a garin na Dapchi.
Dapchi
Bayanan hoto, Lamarin ya faru ne yayin da daliban ke shirin cin abincin dare wasu kuma na shirin sallar Magariba.
Dapchi
Bayanan hoto, Sabbin bayanai na cewa akwai yaro mai suna Mala dan shekara 13 a cikin mutanen da aka sace. Kakan yaron, ya ce dama mahaifin yaron malami ne a makarantar ta Kimiya da Fasaha ta 'yan-Mata da ke garin Dapchi.
Dapchi
Bayanan hoto, A yanzu haka dai Kwalejin ta 'yan-mata zalla na ci gaba da kasancewa a rufe; babu dalibai, babu malamai sai takalma da sauran komatsan da daliban suka watsar a yayin da suke gudun neman tsira.
Dapchi
Bayanan hoto, Kungiyar Boko Haram wacce ake zargi da kai hari a makarantar, har yanzu ba ta ce komai ba, a yayin da batun sace 'yan matan ya janyo sa-in-sa tsakanin Sojoji da 'Yan sanda kan wanda alhakin tsaron makarantar ya rataya a wuyansu.
Dapchi
Bayanan hoto, Malam Tijjani Kalla 'yarsa mai suna Zarah na daya daga cikin dalibai a makarantar ta 'yan mata. Ya yi yunkurin ceto 'yar tasa amma rugugin bindigogi da wulgawar harsasai suka tilasta masa fasa yunkurin nasa.
Dapchi
Bayanan hoto, Tijjani Kalli ya ce dukkanin 'yan makarantar da lamarin ya shafa 'ya'yan talakawa ne, wasu ma marayu ne- ba uwa, ba uba.
Dapchi
Bayanan hoto, Iyayen Zarah sun nuwa wa Wakilin BBC wasu daga cikin litattafan karatunta kuma ga alama daliba ce mai kwazo domin daya daga cikin jarrabawar da aka yi masu ta amsa duka tambayoyin daidai.
Dapchi
Bayanan hoto, Mahaifiyarta ta ce Zarah yarinya ce mai hankali da ilmin boko da na addinin Islama.
Dapchi
Bayanan hoto, Malama Hafsat Juluri daya daga cikin wadanda aka sace 'yarta ta roki gwamnati da ta kara himma domin ceto 'ya'yansu, kuma ta ce tun bayan faruwar al'amarin, "ba mu samu wani bayani daga gwamnati ba, kuma ba wanda ya damu da halin da muke ciki in ban da mutane kamar 'yan jarida."