Hotunan zanga-zangar adawa da kasafin kudi a Nijar

Kungiyoyin fararen hula na adawa da kasafin kudin na 2018 saboda, abin da suka kira takurawa talaka.

Kungiyoyin farar hula sun ce ba su gamsu da kudurin kasafin kudin 2018 na Jamhuriyar Nijar
Bayanan hoto, Kungiyoyin farar hula sun ce ba su gamsu da kudurin kasafin kudin 2018 na Jamhuriyar Nijar ba.
Kungiyoyi na da karfin iko sosai a kasar.
Bayanan hoto, Kungiyoyi na da karfin iko sosai a kasar.
Wannan ne karo na 4 da kungiyoyin ke hitowa dan nuna kin amincewar su ga kasafin kudin shekarar 2018.
Bayanan hoto, Wannan ne karo na hudu da kungiyoyin ke fitowa dan nuna kin amincewarsu ga kasafin kudin shekarar 2018.
Sun yi tur da shirin da gwamnati ke yi na karbar wani kaso a cikin kudin magada
Bayanan hoto, Sun yi tur da shirin da gwamnati ke yi na karbar wani kaso a cikin kudin magada.
Kungiyoyin sun yi gangamin ne tare da hadin gwiwar jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar
Bayanan hoto, Kungiyoyin sun yi gangamin ne tare da hadin gwiwar jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar.
'Yan majalisar dokokin sun ce za su duba batun
Bayanan hoto, 'Yan majalisar dokokin sun ce za su duba batun.
'Yan kasar ta Nijar sun sha kokawa kan matsin halin rayuwa
Bayanan hoto, 'Yan kasar ta Nijar sun sha kokawa kan matsin halin rayuwa.
Kasar na fama da matsalolin rashin tsaro
Bayanan hoto, Kasar na fama da matsalolin rashin tsaro.
Masu gangamin sun ce ba za su daina fafutika ba
Bayanan hoto, Masu gangamin sun ce ba za su daina fafutika ba sai bukatunsu sun biya.