Adikon zamani: Ko me ke sa wasu mata karuwanci?

Bayanan sautiAdikon zamani: Ko me ke sa mata karuwanci?

Adikon zamani: Filin ya tattauna a kan dalilin da suke saka wasu mata shiga karuwanci.

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron shirin tare da Fatima Zahra Umar:

Salamatu (ba shi ne ainihin sunanta ba) matashiya ce mai shekara 22, kyakkyawa ce idan ka kalleta ba za ka taba tsammanin za ta iya yin karuwanci ba.

Salamatu na zaune a Kano, a Abedi da ke cikin Sabon gari, da rana ta na da kamun kai da kamala, amma da daddare sai ta rikide ta koma 'yarinya 'yar harka'.

Na zauna mun tattauna da Salamatu don na yi kokarin gano musabbabin da ya jefa matashiyar kyakkyawa cikin wannna mummunar dabi'a.

Ta shaida min cewa ita daga karamar hukumar doguwa take da ke jihar Kano, kuma ta zo Abedi ne don guje wa auren dole.

Baban ta ne ya aurar da ita ga wani abokinsa mai shekara 69, Alhali kuma ta na da wanda ta ke so.

Ta yi kokarin mijinta ya saketa amma sai yaki, a wannan lokacin ne ta yanke shawarar guduwa da daddare inda ta isa Abedi a Kano.

Ta ce."A lokacin da na je, na zauna da wasu 'yan mata wadan da suka koya min yadda ake sana'ar, da yadda zan yi kwalliya, da irin kayan da zan saka, da kuma yadda zan karbi namijin da ya zo. Babu wanda ya san daga inda na fito, saboda haka abu ne mai sauki na sake da maza. Wani lokacin ina tunanin koma wa gida amma a wannan lokacin na san iyayena ba za su karbeni ba. Wasu lokutan ina jin bakin ciki, amma kuma nan da nan sai na ware na ce ai wannan wani abu ne na dan wani lokaci. Zan dai na nayi aure kwanan nan".

Na tambayeta game da kalubalen da suke fuskanta a sana'arsu, inda ta ce,"Babban kalubalen da suke fuskanta shi ne kamuwa da cutar HIV daga wurin mazan da suke mu'amala da su wadan da ba sa son yin amfani da kwaroron roba. Wata babbar matsalar kuma da suke fuskanta shi ne talauci da yunwa."

Rayuwarta ta sha bam-bam da irin wacce matan karkar suke tunani.

Rayuwa ce mai cike da wahalhalu da suka hada da biyan kudin haya kullum, ko kuma ka kwana da namiji don ya siya maka abinci.

Ta ce, " A wani lokacin ana yin garkuwa da mu, akwai kawayena da dama da aka sace su kuma har yanzu ko labarinsu ba a ji ba, wasu ma anyi tsafi da su, wasu lokutan ma 'yan sanda suna kamasu suyi musu fyade ba tare da dalili ba."

"Wannan rayuwa ce ta kaskanci da wulakanci, ina ga ba zan ba wa wata yarinya shawara a kan ta tsoma kanta a cikin irin wannann rayuwar ba." In ji Salamatu.