'Har yanzu PDP ba ta koyi darasi ba'
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don jin hira da Dr Abubakar Kari:
Masana harkokin siyasar Nigeria sun ce har yanzu jam'iyyar hamayya ta PDP ba ta koyi darasi ba tun zaben da ta sha kaye a shekarar 2015.
Dr Abubakar Kari, Malamin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja da ke Najeriya ne ya bayyana hakan a hirarsa da BBC.