Hotunan filaye 12 da za a fafata a cikinsu a Gasar Russia 2018

A badi ne kasar Rasha za ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya. Ga jerin filayen wasanni 12 da kasashe 32 za su fafata a cikinsu yayin gasar.

Filin wasa na Luzhniki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Luzhniki wanda yake daukar 'yan kallo 81,006 yana birnin Moscow ne kuma an fara bude shi ne a shekarar 1956. Wannan filin shi ne mafi girma a kasar.
Filin wasa na Spartak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Spartak wanda yake daukar 'yan kallo 43,298 yana birnin Moscow ne kuma an fara bude shi ne a shekarar 2014
Filin wasa na Nizhny Novgorod

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Nizhny Novgorod wanda yake daukar 'yan kallo 45,331 yana gabashin birnin Moscow ne kuma za a kammala aikinsa ne a shekarar 2018
Filin Wasa na Mordovia Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Mordovia Arena, wanda yake daukar 'yan kallo 44,442 yana birnin Saransk ne kuma za a kammala aikinsa ne a shekarar 2018
Filin wasa na Kazan Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Kazan Arena, wanda yake daukar 'yan kallo 44,779 yana birnin Kazan ne kuma an fara bude shi ne a shekarar 2013
Filin wasa na Samara Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Samara Arena, zai dauki 'yan kallo 44,807 yana birnin Samara ne kuma za a fara amfani da shi ne a shekarar 2018
Filin wasa na Ekaterinburg Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Ekaterinburg Arena, wanda yake daukar 'yan kallo 35, 696 yana birnin Ekaterinburg ne kuma an fara amfani da shi ne a shekarar 1953
Filin wasa na Saint Petersburg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Saint Petersburg , yana daukar 'yan kallo 68,134 yana birnin Saint Petersburg ne kuma an fara amfani da shi ne a shekarar 2017
Filin wasa na Kaliningrad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Kaliningrad, wanda yake daukar 'yan kallo 35, 212 yana birnin Kaliningrad ne kuma za a fara amfani da shi ne a shekarar 2018
Filin wasa na Volgograd Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Volgograd Arena, wanda yake daukar 'yan kallo 45,568 yana kudu maso yammacin kasar Rasha ne kuma za a fara amfani da shi ne a shekarar 2018
Filin wasa na Rostov Arena

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Rostov Arena, wanda yake daukar 'yan kallo 45,145 yana kudancin birnin Moscow ne kuma za a fara amfani da shi ne a shekarar 2018
Filin wasa na Fisht

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa na Fisht, wanda yake daukar 'yan kallo 47,700 yana birnin Sochi ne kuma an fara amfani da shi ne a shekarar 2013