Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassan Najeriya daban-daban a makon jiya.

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar AtikuBagudu tare da Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya Mai Kanti Baru, bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniyar samar da makamashi daga rake a Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Kebbi State Goverment

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu tare da Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya, Mai Kanti Baru, bayan sanya hannu a kan wata yarjejeniyar samar da makamashi daga rake a Abuja ranar Alhamis
Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yayin da yake sanya hannu a littafin ta'aziyyar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alex Ekwueme a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Marigayin ya rasu ne a Landan a farkon makon jiya.

Asalin hoton, Kaduna State Goverment

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yayin da yake sanya hannu a littafin ta'aziyyar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alex Ekwueme a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Marigayin ya rasu ne a Landan a farkon makon jiya.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da yake duba wani aiki a Jami'ar jihar Borno ranar Laraba

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da yake duba wani aiki a Jami'ar jihar Borno ranar Laraba
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Benin, Omo N' Oba Uku Akpolokpo Ewuare II, a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Benin, Omo N' Oba Uku Akpolokpo Ewuare II, a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis
Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yayin da ya halarci taron yaye dalibai a cibiyar nazarin manufofi da muhimman bukatu ta kasa (NIPSS) a Kuru kusa da Jos ranar Asabar

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yayin da ya halarci taron yaye dalibai a cibiyar nazarin manufofi da muhimman bukatu ta kasa (NIPSS) a Kuru kusa da Jos ranar Asabar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya gana da shugabanin Musulmi 'yan darika a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya gana da shugabanin Musulmi 'yan darika a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwanbo da Aminu Tambuwal na jihar Sakkawato da kuma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a zauren taron ba da kyautukan yabo wanda jaridar New Telegraph ta shirya a jihar Legas ranar Asabar

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkawato da kuma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a zauren taron ba da kyautukan yabo wanda jaridar New Telegraph ta shirya a jihar Legas ranar Asabar
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mai dakinsa, bayan ya karbi kyautar gwarzon gwamna a bangaren kiwon lafiya da samar da ilimi wanda jaridar New Telegraph ta ba shi a Lagos ranar Asabar

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mai dakinsa, bayan ya karbi kyautar gwarzon gwamna a bangaren kiwon lafiya da samar da ilimi wanda jaridar New Telegraph ta ba shi a Lagos ranar Asabar