Hotunan yadda 'yan Shi'a suka yi zanga-zanga a Abuja

'Yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja domin neman gwamnati ta saki malamin.

Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, 'Yan kungiyar 'yan uwa Musulmi dai suna neman a sakar musu Sheikh Ibrahim Zakzaky ne
Zakzaky
Bayanan hoto, Magoya bayan malamin suna nema a sake shi domin ya samu kyakkyawar kulawa
Sheikh Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, Sun ce ba su yarda da yadda gwamnatin Najeriya take ci gaba da rike jagoransu ba
Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, Sun ce ba su yarda da kwamitin da gwamnati ta kafa domin binciken abin da ya faru tsakaninsu da jami'an tsaro ya zauna a asirce ba
Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun ce ba za su daina gangami ba sai an sako malaminsu
Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, An kama Sheikh Ibrahim Zakzaky ne bayan an yi arangama tsakanin mabiyansa da jami'an tsaro a shekarar 2015
Ibrahim Zakzaky
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar suna son a bar shugabansu ya yi jawabi a bainar jama'a