Kun san yadda ake zabar shugaban China?
Ana gudanar da babban taron jam'iyyar kwaminisanci ta China NCCPC karo na 19 .
Taro ne na manyan shugabannin jam'iyyar wadanda za su yanke hukunci kan mukaman gwamnati, kuma ana yin zaben ne sau biyu a shekara.
Yayin da ake sa ran Xi Jinping zai yi ta zarce a matsayin shugaban jam'iyyar, akwai yiwuwar cewa za a samu manyan sauye-sauye a shugabancin jam'iyyar da za su yi ritaya.