Iraq: Wai ina mayakan IS suka gudu ne?
Dakarun Iraki da mayakan sa kai na Shi'a sun fatattaki mayakan IS daga garin Hawija, wanda yana daya daga garuruwan da a baya ke karkashin ikon IS din a kasar.
Tun lokacin da aka fara gumurzun dubban fararen hula suka tsere daga birnin, da suka hada da daruruwan mazan da ake zaton mayakan IS ne.