Hotunan 'motocin' da ke tashi sama a Dubai

An fara gwajin motocin tasi marasa matuka wadanda za su rika tashi sama a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Motoci masu tashi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Motar wadda za ta rika daukar fasinja biyu, ta yi tafiyar minti 15 ne yayin gwajin farko a makon jiya
Motoci masu tashi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani kamfanin Volocopter na kasar Jamus wanda yake kera jirage marasa matuka ne ya kera tasin
Motoci masu tashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Motar wadda take amfani da wutar lantarki, za ta rika tafiyar minti 30 ne kawai, bisa gudun kilomita 25 a tsawon minti 30
Motoci masu tashi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An fara gwada tasin ne a Jamus a watan Afrilun bana
Motoci masu tashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi gwajin tasin ne a unguwar Jumeirah ta gabar teku kuma za a fara amfani da su ne nan da shekara biyar masu zuwa