Nigeria: Kun san asarar da aka tafka a rikicin IPOB?

Bayanan sautiKarin bayanin da wakilinmu Abdussalam Ibrahim Ahmed ya yi kan asarar da 'yan arewa suka tafka asara a rikicin IPOB

'Yan arewacin Najeriya da ke zaune a kudu maso gabashin kasar sun ce sun tafka asarar rayuka da ta dukiya sakamakon rikicin da masu fafutikar kafa kasar Biafra suke yi a yankin.

Sun shaida wa wakilinmu na yankin Abdussalam Ibrahim Ahmed cewa an kashe mutanensu da dama da kuma kona dukiyarsu.

Sai dai jami'an tsaro sun ce ba a samu asarar rayuka ba kawo yanzu.