Kalli bidiyon ziyarar da Yemi Osinbajo ya kai wa Buhari
Kalli bidiyon lokacin da Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bar wurin da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a London.
Wannan ne karon farko da shugabannin biyu suka gana tun bayan da Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar domin jinya a London sama da wata biyu.
A farkon shekarar nan ma shugaban ya je jinyar London inda ya shafe kusan wata biyu.
Ba a dai bayyana takamaiman abin da ke damunsa ba.