Yadda ambaliya ta yi raga-raga da gidaje kusa da Abuja

BBC ta ziyarci anguwannin da ambaliyar ruwa ta kashe mutane tare da lalalce kadarori, ta dauko hotunan yadda ibtila'in ya yi da wurin.

Suleja Flood
Bayanan hoto, Yara na wasa kan baraguzan wasu gidajen da ambaliyar ta lalata.
Suleja Flood
Bayanan hoto, Yara suna ta wasa da wanka cikin daya daga cikin wuraren da ambaliyar ta faru.
Suleja Flood
Bayanan hoto, Wata mata na wucewa gefen wani gidan da ambaliyar ta rushe baki daya
Suleja Flood
Bayanan hoto, Wata mota na kokarin dilmiyewa a cikin ruwa
Suleja Flood
Bayanan hoto, Wani mutum na kallon yadda ambaliyar ta yi da wata katanga
Suleja Flood
Bayanan hoto, Yara na tsince-tsince cikin ruwan
Suleja Flood
Bayanan hoto, Wasu daga cikin kayayyakin aikin cikin gida na wasu wadanda lamarin ya shafa
Suleja Flood
Bayanan hoto, Mutane na fitar abubuwan da za su iya cetowa daga baraguzan ginin
Suleja Flood
Bayanan hoto, Nan ma wasu ne ke kokarin cire abubuwa masu amfani da za su iya fitarwa
Suleja Flood
Bayanan hoto, Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su
Suleja Flood
Bayanan hoto, Mutane na tafiya a hanakali cikin baraguzan gidajen da lamarin ya shafa