Ganawar Buhari da 'yan matan Chibok a hotuna

Shugaba Buhari ya gana da 'yan matan Chibok 82 da aka ceto a ranar Lahadi, jim kadan kafin ya London ganin likita. Ga abin da ya gaya musu cikin hotuna.

'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, A ganawar da ya yi da 'yan matan, shugaba Buhari ya ce ba zai iya bayyana tsantsar farin cikin da yake ciki ba na yi wa wadannan 'yan mata maraba da dawowa cikin iyalansu da kuma samun 'yancinsu.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, "Dama mun sha fada cewa za mu yi duk abin da za mu iya don ganin yaran nan da ma sauran mutanen da ke hannun mayakan Boko Haram sun dawo lafiya," in ji Shugaba Buhari.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, Shugaban ya tabbatarwa da 'yan matan cewa fadar shugaban kasa ce da kanta za ta sa ido kan wadanda aka damkawa amanar kula da 'yan matan ta fannin lafiyarsu da iliminsu da tsaronsu da duk wani abu da suke bukata.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, Ya kuma godewa kungiyoyi da kasashen da suka shiga cikin tattaunawar da aka yi da mayakan Boko Haram din don karbo 'yan matan.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, A yayin da suke ganawa da jami'an gwamnati, alamu sun nuna cewa wasu daga cikin 'yan matan a gajiye suke sosai.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, Bayan ganawarsu da shugaban ne kuma aka kai su wata cibiyar lafiya don duba lafiyarsu da ba su taimakon da ya dace.
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya kara da cewa, “Bari na tabbatarwa da 'yan Najeriya, musamman ma 'yan uwa da iyayen sauran 'yan matan da ba a gani ba cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba don ganin an ceto duk wasu 'yan Najeriya da ke hannun kungiyar Boko Haram, don su ma su samu 'yancinsu."
'Yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, 'Yan matan da aka ceto din na cikin walwala da farin ciki, sun kuma nuna godiyarsu ga Allah da gwamnatin Najeriya.