Kalli bidiyon 'yan matan Chibok da aka ceto
Bidiyon 'yan matan Chibok na Najeriya da Boko Haram ta sako bayan shafe shekara uku a hannunta sakamakon musayar fursunonin da gwamnati ta yi da su.
An sako 'yan matan 82 ne sakamakon yarjejeniyar da aka kulla wacce kungiyar agaji ta ICRC ta shiga tsakani.
Har yanzu akwai wasu 'yan matan fiye da 100 a hannun mayakan.