Ku kalli hotunan ma'aikatan BBC na London da wakilanta na shiyya

Albarkacin cikar BBC Hausa shekara 60 da fara watsa shirye-shirye, ga kundin hotunan ma'aikatan London da wakilanmu na shiyya da lokutan da suka fara aiki.

Jimeh Saleh
Bayanan hoto, Jimeh Saleh shi ne mukaddashin shugaban sashen Hausa na BBC. Jimeh ya fara aiki da BBC a shekarar 2008.
Ahmad Abba Abdullahi
Bayanan hoto, Ahmad Abba Abdullahi ya fara aiki da BBC ne a shekarar 1995.
Sulaiman Ibrahim Katsina
Bayanan hoto, Sulaiman Ibrahim Katsina tsohon hannu ne a BBC, ya fara aiki da BBC Hausa tun shekarar 1987, shekararsa 30 kenan a bana.
Mijinyawa da Coulibaly
Bayanan hoto, Ibrahim Mijinyawa daga hagu wanda ya fara aiki a shekarar 2007, shi kuwa Alhadji Coulibali (daga hannun dama) ya fara ne a shekarar 1998.
Suwaiba and Aichatou
Bayanan hoto, Suwaiba Ahmad daga hagu, da Aichatou Moussa daga dama. Suwaiba ta fara aiki da BBC a shekarar 2004 da ita aka bude ofishin Abuja daga bisani ta koma London. Aichatou kuwa ta fara aiki da BBc ne a shekarar 1998.
Aliyu Abdullahi Tanko
Bayanan hoto, Aliyu Abdullahi Tanko ya fara aiki ne da BBC a shekarar 2008. A yanzu haka kuma yana aiki na wucin gadi da wani sashen Turanci domin kara sanin makamar aiki.
Aminu Abdulkadir Kado
Bayanan hoto, Aminu Abdulkadir Kado
Raliya da Bara'atu
Bayanan hoto, Raliya Zubairu (daga hagu) ta fara aiki da BBC a shekarar 2008, yayin da Bara'atu Ibrahim (daga dama) ta fara aiki a watan Fabrairun 2015. Raliya ma'aikaciyar ofishin Abuja ce, amma ta je London sanin makamar aiki na wucin gadi.
Haruna Shehu Mararrabar-Jos
Bayanan hoto, Haruna Shehu Mararrabar-Jos ya fara aiki da BBC ne a watan Mayun 2014.
Ibrahim Shehu Adamu
Bayanan hoto, Ibrahim Shehu Adamu ya fara aiki da BBC Hausa a shekarar 2009, a yanzu haka kuma yana aikin wucin gadi da wani sashen Turanci don kara sanin makamar aiki.
Ishaq Khalid
Bayanan hoto, Ishaq Khalid shi ne wakilin BBC a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. A yanzu yana ofishinmu na London don yin aikin wucin gadi don kara kwarewa a sanin makamar aiki. Ya fara aiki a shekarar 2010.
Baro Arzika
Bayanan hoto, Baro Arzika shi ne wakilin BBC a Yamai, Jamhuriyyar Nijar. Ya fara aiki da BBC a ranar 18 ga watan Janairun 2010.
Yusuf Ibrahim Yakasai
Bayanan hoto, Wakilin BBC Hausa na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, wanda yake Kano, wato Yusuf Ibrahim Yakasai kenan. Ya fara aiki da BBC a watan disambar 2009.
AbdusSalam Ibrahim Ahmad
Bayanan hoto, AbdusSalam Ibrahim Ahmad kenan, wakilin BBC a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya. Ya fara aiki tun shekarar 1999.
Tchima Ila Issoufou
Bayanan hoto, Tchima Ila Issoufou ita ce wakiliyar BBC a Damagaram ta jamhuriyyar Nijar. ta fara aiki da BBC a watan Satumbar 2009.
Nura Muhammad Ringim
Bayanan hoto, Wannan shi ne Nura Muhammad Ringim. Wakilin BBC na Kaduna a Najeriya. Nura ya fara aiki ne a shekarar 2007.
Elleman
Bayanan hoto, Umar Shehu Elleman shi ne wakilin BBC da ke Lagos a Kudu maso Yammacin Najeriya, ya kuma fara aiki da sashen ne a shekarar 2006.
Muhammad Fahad Adam
Bayanan hoto, Muhammad Fahad Adam ne wakilin BBC a Ghana. Ya fara aiki da BBC Hausa a shekarar 2016.